
15 Fabrairu 2024
Crystal Palace na shirin korar kocinta Roy Hodgson, kuma ana s ran kungiyar ta maye gurbinsa da tsohon kocin Eintracht Frankfurt, Oliver Glasner.
Ƙungiyar Eagles na matsayi na 15 yanzu haka a kan teburin Premier, kuma maki biyar ne ke tsakaninta da ƙungiyoyi ukun ƙarshe.
Ya kamata a ce Hodgson ya yi taron manema labarai a yau Alhamis, amma Palace ta soke shi, tana cewa "ya samu rashin lafiya a yayin atisayen da aka yi yau da safe".
Palace za ta fafata da Everton a Goodson Park a gasar Premier a ranar Litinin.
Kocin mai shekara 76, ya ja ragamar ƙungiyarsa a wasanni 200 a matsayin koci a farkon wannan makon, sai dai sun yi rashin sa'a, bayan da Chelsea ta doke su da ci 3-1 a filin wasa na Selhurst Park.
Wasanni uku kacal ƙungiyar ta ci tun nasarar da ta yi a kan Manchester United a watan Satumbar bara, kuma ta yi rashin nasarar wasa 10 cikin 16 da ta buga.
wannan ne karo na biyu da tsohon kocin Ingilan ya ke jan ragamar Palace, ya koma a bara saura wasanni 10 kakar ta ƙare, lokacin da ya sanya hannu kan kwantaragin ƙanƙanin lokaci, inda ya maye gurbin Patrick Vieira.
Ya mayar da ƙungiyar matsayi na 11 kafin ya amince ya ci gaba da jagorancinta a kakar 2023-24.
Magoya baya sun riƙa ɗaga kwalaye suna neman a kori Hodgson sun bayyana damuwarsu kan yadda ƙungiyar ke samun koma baya.
ncG1vNJzZmivp6x7o67CZ5qopV%2Bdrra%2FwGiYq6yZmLmmv46caLBpaa7GuIOWr6Y%3D